Watan Sha aban

 WATAN SHA'ABAN 🌾


Shaykh Sulaiman Ar-Ruhaili yake cewa: "Ya ku masoyana ina muku kashedi game da Allah, ku kiyayi Allah, hakika Allah ya muku ni'ima da ya sanya ku cikin wadanda suka riski wannan watan na sha'aban alhali kuna cikin koshin lafiya da karfi da alkhairi, dan haka ku godewa Allah mai girma da daukaka abisa wannan ni'imar da ya muku, ku kyautatawa kanku ta hanyar yawaita azumi awannan watan, la'alla Allah ya sanyaku cikin wadanda zasu samu aljannah adalilin azumtar wannan watan da kuka yi  kuma ya ƴantar daku daga wuta. 

    Ya ku bayin Allah ina muku gargadi da kashe di game da Allah abisa wannan ganimar da ya baku, kada ku yi sakaci da ita, kada ku yi kasala acikinta, ku yi rige rige acikinta wurin aikin alkhairi, ku sani abun sayarwar tanada tsada, hakika abun sayarwar Allah shi ne aljannah, kuma tabbas kudin sayanta da ake nema awurinku dan kadanne yaku bayin Allah".


خطبة يوم الجمعة ١٤٣٨/٨/١هـ

Comments

Popular posts from this blog

DISCIPLINE AND KNOWLEDGE